A nasa bangare, kwamitin dake nemawa birnin Beijing wannan matsayi ya fidda sanarwa dake cewa Sin na matukar farin ciki da samun wannan dama, kuma tana godiya bisa amincewar da kwamitin na IOC ya nuna mata, da taimakon da kungiyoyi masu kula da wasannin motsa jiki na kasa da kasa suka bayar. Kaza lika kwamitin ya godewa kafofin yada labaru na gida da na waje, wadanda suka zura ido kan lamarin, tare da dukkanin jama'ar kasar Sin dake gida da waje. A sa'i daya kuma, kwamitin ya jinjinawa birnin Alma-Ata na kasar Kazakhstan wanda shi ma ya nemi wannan matsayi, tare da darajanta kokarin da ya yi.
Ban da wannan kuma, sanarwar ta ce a matsayin birni wanda ya taba daukar bakuncin wasan Olympic na yanayin zafi, birnin Beijing zai dauki nauyin shirya wasan Olympic a yanayin sanyi na shekarar 2022, zai kuma cika alkawarinsa, game da shirya wannan gasa yadda ya kamata a daidai lokacin bikin bazara na gargajiyar kasar Sin a shekarar ta 2022.
Bugu da kari birnin Beijing na maraba ga daukacin al'ummar duniya da zuwa birnin Beijing a shekarar 2022 don a hadu a wannan gaggarumar gasa . (Amina)