Mr. Thomas ya bayyana hakan ne a birnin Kuala Lumpur na kasar Maleshiya, yana mai cewa don haka birnin na Beijing ne zai kasance birni daya tak a duniya, wanda ya samu damar shirya gasar Olympics a yanayin zafi da yanayin sanyi baki daya.
A shekarar 2008 ne dai birnin Beijing ya gudanar da gasar wasannin Olympics na yanayin zafi karo na 29, tare da cimma gagarumar nasara. A wannan karo kuma, zai yi hadin gwiwa tare da birnin Zhangjiakou, wajen shirya wata babbar gasar wasannin Olympics. Bisa jimilla an kiyasta cewa, za a kashe kudi dala biliyan 1.5 wajen gudanar da wannan gasa.(Fatima)