Yayin ganawar, Mr. Wang ya ce, tun hayewa kujerarsa, Mr. Bach ya yi iyakacin kokarin gudanar da ayyukan kirkire-kirkire don sa kaimi ga wasannin motsa jiki na Olympic.
Ban da wannan kuma, Mr. Wang ya ce, birnin Beijing da na Zhangjiakou na Sin na kokarin neman daukar nauyin shirya wasannin Olympic na yanayin hunturu na shekarar 2022, da zummar sa kaimi ga miliyoyin Sinawa da su shiga ayyukan motsa jiki, matakin da zai yada tunanin Olympic da wasannin motsa jiki irin wanda aka yi a kan dusar kankara. Sin a nata bangare na da karfi kuma ta cancanta ta dauki nauyin shirya wannan gasa.
A nashi bangare, Mr. Bach ya ce, kwamitinsa na darajanta tunanin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dauka na baiwa jama'ar kasar kwarin gwiwar yin motsa jiki. Kwamitin kuma ya hada kai da Sin cikin dogon lokaci, yana fatan za a inganta hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu nan gaba. (Amina)