in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugaban kungiyar kwamitin shirya gasar wasannin Olympics
2015-01-14 20:40:50 cri
A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kungiyar kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na kasa da kasa da shiyya-shiyya, kana shugaban hukumar wasannin Olympic na Asiya yarima Ahmad Al-Fahad Al-Sabah a nan birnin Beijing.

A yayin ganawarsu, Xi Jinping ya ce, a kullum gwamnatin kasar Sin na dukufa kan raya harkokin wasannin motsa jiki, kana wasannin Olympic na da muhimmanci ga bunkasuwar zamantakewar al'umma. Cikin 'yan shekarun nan, kasar Sin ta yi nasarar shirya gasar wasannin Olympic da ya gudana a Beijing da kuma gasar wasannin Olympic ta matasa da aka yi a birnin Nanjing da dai sauransu, wadanda suka kara sha'awar jama'ar kasar Sin kan wasannin Olympic sosai.

Xi Jinping ya jaddada cewa, birnin Beijing da birnin Zhangjiakou sun gabatar da takardar neman iznin shirya gasar wasannin Olympic ta lokacin sanyi karo na 24 na shekarar 2022. Idan har birnin Beijing ya samu nasarar shirya gasar wasannin Olympic ta lokacin sanyi wannan zai iya sa kaimi ga jama'ar kasar sama da miliyan dari uku su kalli wasannin zamiyar kankara, wannan zai taimaka ga bunkasuwar gasar wasannin Olympic ta kasa da kasa.

A nasa bangaren yarima Ahmad Al-Fahad Al-Sabah ya ce, cikin 'yan shekarun nan, hukumomin wasannin motsa jiki na kasa da kasa sun cimma nasarori da dama wajen shirya manyan gasar wasanni a kasar Sin bisa hadin gwiwarsu da kasar Sin, don haka suna godiya matuka ga gwamnatin kasar Sin bisa ga goyon bayan da ta bayar game da bunkasuwar harkokin wasannin motsa jiki, kuma yana fatan alheri ga biranen Beijing da Zhangjiakou kan neman izinin karbar bakuncin gasar wasannin Olympic ta lokacin sanyi karo na 24. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China