in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe gasar wasannin Olympics ta matasa a birnin Nanjing na Sin
2014-08-28 21:38:36 cri

Yau da dare, bisa agogon Beijng ne aka rufe gasar wasannin Olympics ta matasa ta lokacin zafi karo na biyu a birnin Nanjing na kasar Sin.

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci bikin rufe gasar. Thomas Bach, shugaban kwamitin shirya gasar wasan Olympics ta kasa da kasa shi ne ya sanar da rufe gasar. Za a yi gasar karo na uku a birnin Buenos Aires, hedkwatar kasar Argentina.

'Yan wasa sama da 3700 da suka zo daga kasashe daban-daban ne suka halarci wasannin guda 222 da aka fafata a kansu, inda aka kashe kwanaki 12 ana yinsu, a sa'i daya kuma, an gudanar da wasu shirye-shiryen al'adun da abin ya shafa a yayin gasar, inda matasan kasa da kasa suka shiga cikin wasannin motsa jiki cikin himma da kwazo, inda suke yin cudanya da juna tare da bin akidar gasar ta Olympics.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China