in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya mika sakon godiya ga kwamitin IOC
2015-07-31 19:59:56 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon godiya ga shugaban kwamitin shirya gasar Olympic na kasa da kasa Mr. Thomas Bach. Cikin sakon wanda aka mika ga Mr. Bach da yammacin Juma'ar nan, shugaba Xi ya jinjinawa kwamitin IOC bisa amincewa da kuma goyon baya da ya baiwa kasar Sin, wadda aka baiwa biranen ta biyu wato Beijing da Zhangjiakou damar karbar bakuncin gasar Olympic ta lokacin sanyi a shekarar 2022 mai zuwa.

A cewar shugaban Xi, bisa burin da ake da shi na shirya gagarumar gasa mai kayatarwa, wadda za ta dace da burin al'ummar Sinawa biliya 1.3, gwamnati za ta cika alkawuran ta, za kuma a cimma babbar nasarar da ake fata da hadin kan dukkanin al'umma, da kuma goyon bayan kasashe, da shi kan sa kwamitin na IOC, ta yadda hakan zai zamo dama ta yada manufar Olympic a duniya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China