in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban tawagar 'yan wasan kasar Nijer ya yabawa da tsarin gasar Olympics ta matasa a birnin Nanjing
2014-08-27 10:42:16 cri
Shugaban tawagar 'yan wasan kasar Nijar, wadanda suke halartar gasar wasannin Olympics ta matasa a birnin Nanjing dake kasar Sin Omar Sungaizai, ya yi matukar yabawa yadda aka shirya sassan wannan gasa.

Sungaizai ya shaidawa wakilinmu cewa, gasar ta gudana cikin nasara, an kuma gudanar da ayyuka daban daban tare da bada hidima mai inganci. Kaza lika a cewar sa an yi amfani da fasahohi da na'urorin zamani wajen gudanar gasar, lamarin da ya burge shi matuka.

Game da nasarorin da tawagar kasar Nijer ta samu sakamakon halartar gasar ta wannan karo, Sungaizai ya ce Nijer ba kasa ce mai arziki ba, don haka, kudin da ta zuba a fannin wasanni ma ba shi da yawa, wanda hakan ya sanya ta gaza samun cikakkiyar nasara a gasanni makamantan wannan.

Sai dai duk da hakan jagoran tawagar ta Nijar ya ce ta hanyar halartar wannan gasa, idon matasan 'yan wasan kasar zasu bude, tare da fahimtar al'adun kasashe daban daban, kana 'yan wasan sun gamsu da yadda gasar ta gudana.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatin kasarsa ta Nijar da sauran kasashen Afirka, da su kara zuba jari a fannin wasanni, yana mai cewa ta hanyar bunkasa sha'anin wasanni, za a iya kara kyautata lafiyar al'umma, da rage kudaden da aka kashewa a fannin kiwon lafiya. Irin kudaden da za a iya amfani da su wajen inganta aikin bada ilimi, da sauran muhimman fannonin bunkasa zamantakewar al'umma. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China