A ranar litinin din nan mahukuntar filin saukar jiragen sama na kasa da kasa dake Geneva na kasar Switzerland suka bayyana cewa mutumin dan shekaru 31 ya kulle kansa a cikin sashin matukan jirgin bayan da ya samu nasarar juya akalar jirgin samfurin 767-300 sannan kuma ya nemi mafaka a kasar ta Switzerland.
Tun da farko dai Jean-Philippe Bramdt,kakakin hukumar 'yan sanda na gundumar Geneva ya shaida ma Xinhua cewa har yanzu ana cigaba da bincike don haka za'a fitar da sauran bayanai da zaran an kammala.
Jirgin saman dai mai lamba ET-702 da ta tashi daga Adis ababa babban birnin kasar Habasha zuwa Milan inda zata yada zango a Rome duka a kasar Italiya an tilasta mata sauka a babban filin jiragen sama na kasa da kasa dake Geneva da misalin karfe 6 na safiyar wannan rana bayan da aka samu labarin yin fashin ta lokacin da ta keta sararin samaniyar kasar Sudan.
'Yan sanda da suka isa filin saukan jiragen sama sun samu nasarar shawo kan al'amarin, abinda Mr. Bramdt yayi bayanin cewa fasinjoji da ma'aikatan jirgin duk suna cikin koshin lafiya sannan kuma an fitar dasu daga cikin jirgin daya bayan daya.
A yanzu haka dai an rufe filin saukan jiragen saman na Geneva har zuwa wani dan lokaci abin da ya sa aka soke saukan jirage a filin.