in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Habasha ya gana da ministan harkokin wajen Sin Wang Yi
2014-01-07 16:11:54 cri

Shugaban kasar Habasha Mulatu Teshome ya gana da ministan harkokin wajen Sin Wang Yi a fadar shugaban kasa da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha a ran 6 ga wata.

A yayin ganawar tasu, Mista Mulatu ya ce, Sin wata kasa ce mai girma. Sin tana ba da taimako sosai ga kasar Habasha a fannonin zuba jari, ayyukan more rayuwar al'umma, makamashi da dai sauransu, take da nuna goyon baya ga Habasha wajen canza hanyoyin da take bi wajen samun bunkasuwar tattalin arziki, kuma wani misali ne ga hadin kai a tsakanin kasashe masu tasowa, kuma kasar Habasha ta nuna godiya matuka ga kasar Sin. Bugu da kari, Habasha ta darajanta dangantakar da ke tsakaninta da Sin, tana son inganta hadin kai a tsakaninta da Sin a fannonin siyasa, da tattalin arziki da cinikayya, da al'adu da dai sauransu, domin kara samar wa juna moriya da jin dadin jama'ar kasashen biyu.

Mista Wang ya yi nuni cewa, har kullum Sin da Habasha suna goyon bayan juna, da taimakwa juna bias tsawon tarihi, ba za a iya raba su da juna ba. Zurfafa yin gyare-gyare da bude kofa ga duniya da Sin ke yi zai samar da muhimmiyar dama ga bunkasuwar Afirka, kuma zai sa kaimi ga hadin kai a tsakanin Sin da Habasha. Sin tana yin kokari tare da Habasha wajen aiwatar da ra'ayi daya da shugabannin bangarorin biyu suka samu domin raya hulda tsakaninsu, tare da tsayawa kan ra'ayin da shugaban Sin Xi Jinping ya gabatar na moriyar juna cikin daidaici, domin samun bunkasuwa tare.

A ran 6 ga wata kuma, firaministan Habasha Haile Mariam shi ma ya gana da Wang Yi a fadarsa da ke a Addis Ababa.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China