in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta mika wa kasar Kamaru cibiyar nazarin fasahar ayyukan noma
2013-07-19 16:51:48 cri
Bisa labarin da aka samu ran 18 ga wata, mukadashin wakilin ofishin jakadancin Sin da ke kasar Kamaru Li Chanlin da ministan kula da harkokin raya kauyuka da ayyukan noma na kasar ta Kamaru Essimi Menye, a madadin gwamnatocin kasashen biyu, sun sa hannu kan takardar mika cibiyar nazarin fasahar ayyukan noma da kasar Sin ta ba da taimakon ginawarta ga kasar Kamaru a Yaounde babban birnin kasar.

Essimi Menye ya bayyana cewa, cibiyar nan da aka gina bisa taimakon kasar Sin muhimmiyar sakamako ce ta ayyukan hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Kamaru, kuma ya yi imani cewa, cibiyar za ta taimaka matuka wajen bunkasar ayyukan noma a kasar Kamaru.

Cibiyar nazarin fasahar ayyukan noma mai fadin kadada dari daya tana birnin Nanga Eboko ne dake lardin tsakiya na kasar Kamaru, kuma kamfanin aikin gona na lardin Shanxi na kasar Sin shi ne ya gina ta da kuma kula da harkokin ayyukanta.

An fara aikin gina cibiyar a watan Yuli na shekarar 2009, har zuwa watan Janairu na shekarar 2011, wato lokaci da aka kammala ayyukan ginawa.

Cibiyar tana daya daga cikin manyan ayyukan Sin wajen gudanar da taimako a fannoni takwas na taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da aka yi a birnin Beijing da kuma sakamakon ziyarar tsohon shugaban Sin Hu Jintao zuwa kasar Kamaru a shekarar 2007. Manufar ginawarta itace don ba da taimako ga kasar Kamaru wajen samar da isasshen abinci, bunkasa ayyukan noma, da kuma kawar da talauci.

Cibiyar na da wuraren aikin ba da horaswa, sarrafa hatsi da kuma gidajen kwana, kana ana da gonakin gwajin shuke-shuke da kuma sarrafa hatsi, ta yadda za a iya cimma burin nazarin ayyukan noma da yin gwaje-gwaje, horaswa a fuskar fasaha da kuma bunkasa ayyukan noma cikin dogon lokaci.(Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China