in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manoma miliyan 600 suna shiga zaben kwamitin manoma
2013-03-13 16:10:05 cri

A safiyar yau Laraba 13 ga wata a gun taron manema labaru da aka yi a cibiyar watsa labaru ta taro na farko na majalisar wakilai na 12 na jama'ar kasar Sin, mataimakiyar ministan hukuma mai kula da harkokin al'umma Jiang Li ta nuna cewa, yin zabe a dimokuradiyya ce ba ma a kauyen Wu Kan kawai ba a nan kasar Sin aka yi shi, kauyuka da dama sun yi irin wannan zabe wanda ya zama tamkar matakin da ake dauka wajen kyautata tsarin siyasa irin na gurguzu na kasar Sin.

Ta bayyana cewa, yanzu haka, kauyuka kashi 98 bisa dari sun gudanar da zabe kai tsaye, kuma yawan manoma da suka shiga zaben ya kai kashi 95 cikin dari. Ana yin zaben kwamitin manoma a wannan karo da aka fara daga shekarar 2011 zuwa ta 2013, manoma da yawansu ya kai miliyan 600 za su shiga zabe, abin da ya sa irin wannan zabe ya samu halartar mutane mafi yawa a duniya.

Jiang Li ta ce, yin zabe a dimokuradiyyace ya zama wani muhimmin mataki ne wajen gina tsarin siyasa mai tushe a kauyuka a kasar Sin. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China