A jiya Talata ne kasar Sin ta kammala wani taro na yini biyu game da tsarin inganta yankunan karkara, inda ta lashi takwabin kara zamanantar da aikin gona ta hanyar yin kwaskwarima da kirkire-kirkire.
Wata sanarwa da aka bayar bayan wannan taro ya nuna irin ci gaban da kasar Sin ta samu a aikin raya yankunan karkara a shekara ta 2014, da wata nasarar a fannin samun amfanin gona sau 11 a jere, lamarin da ya kara samar da kudaden shiga ga manoma.
Sanarwar ta ce, muddin kasar Sin tana bukatar samun ci gaba mai dorewa a bangaren aikin gona, wajibi ne ta shirya tunkarar wasu kalubale da za su kunno kai, kamar karuwar kudaden gudanar da aikin gona, karancin filaye noma da ruwa da sauransu.
Masana a taron sun bayyana kudurinsu na kokarin hanzarta zamanantar da bangaren na noma, ta yadda za a kara samar da abinci tare da bude hanyoyin zuba jari a bangaren samar da kayayyakin more rayuwa a yankunan karkara.
Taron na bana ya tattauna yadda za a zurfafa yin kwaskwarima a yankunan karkara da kuma zamanantar da bangaren aikin gona.
Manufar taron da aka saba gudanarwa shekara-shekara ita ce tattaunawa tare da tsara manufofi kan yadda za a raya yankunan karkara a shekara mai zuwa. (Ibrahim)