Yayin taron, an tabbatar da cewa, za a fara gwajin aikin gyare-gyaren na tsarin noman zamani a wasu wuraren da suka fi dacewa.
Manyan ayyukammu su ne, sabunta tsarin tafiyar da sha'anin noma, karfafa gyare-gyaren tsarin gudanar da gonaki, bin manufofi daban daban wajen yin amfani da gonaki bisa yanayinsu don bunkasa ayyukan noma na zamani, da kuma kyautata aikin hidima a fannin sha'anin kudi ta yadda za a kara zuba jari a yankunan karkara daga fannoni daban daban.
Banda wadannan kuma za a kyautata tsarin sabunta kimiyya da fasahar ayyukan noma da yin hidimomin ayyukan, karfafa tsarin ba da horaswa ga manoma, inganta ayyukan ban ruwa da aikin gyare-gyaren tsarin gudanar da ayyukan, kara sauran yunkurin dunkulewa tsakanin birane da karkara, kana a mai da hankali wajen kiyaye wayin kan sha'anin noma da al'adun karkarar Sin, da kuma neman sabbin hanyoyin da za su dace wajen bunkasa birane da karkarar izuwa na zamani bisa daidaici. (Maryam)