in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firimiyan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada muhimmancin tsarin noma na zamani
2013-03-31 16:39:42 cri

Yayin wata ziyarar aiki da ya gudanar a yankin fadamar dake dab da kogin Yangtze, Firimiyan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada bukatar dake akwai, ta habaka harkokin noma irin na zamani.

Haka zalika yayin ziyarar, Li Keqiang ya bayyana farin cikinsa, ganin yadda kananan manoman dake Changshu, a lardin Jiangsu dake Gabashin kasar suka samu karin bunkasuwa, ta fuskar yawan hatsin da suke nomawa, karkashin shirin dunkule gonakinsu, da fadada tsarin noma, ta yadda a yanzu suke iya amfani da sabon tsarin fasahar noma a sana'ar tasu.

A cewarsa, tsarin hadin gwiwa tsakanin masu mallakar kananan gonaki, da kulla dangantaka tsakanin kungiyoyin gama kai, na cikin manyan hanyoyin bunkasa aikin noma da kasar Sin ke bukata.

Wannan dai tsokaci na Firimiya Li Keqiang, na zuwa ne daidai gabar da kasar ta Sin ke ci gaba da rungumar sabon tsarin amfani da filayen noma, dake bada damar habaka ribar manoma, dama ikon daga matsayin sana'ar ta noma zuwa mataki na gaba a dukkanin fadin kasar.

Sabanin tsarin mallakar filayen noma na da, a yanzu haka sashen kundi na daya, na dokokin gwamnatin tsakiya na wannan shekara ta 2013, wanda ke baiwa bukatun al'ummomin yankunan karkara kulawa ta musamman, ya tanadi sabon tsarin mallakar filayen noma, wanda ke kunshe da baiwa manoma kwarin gwiwar hadin gwiwa da juna, ta yadda zasu bunkasa sana'ar su. Haka zalika tsarin, zai samar da dama ga manoman, ta habaka ayyukan kwadago da gonakin nasu ke bukata, matakin da a cewar Firimiya Li Keqiang, yayi daidai da manufar gwanmati, ta gaggauta fadada biranen kasar. A hannu guda Firimiyan ya tabbatar da cewa, yayin da ake daukar matakan bunkasa sashen na noma, za kuma a ci gaba da tabbatar da kare hakkin kananan manoman kasar baki daya.(Saminu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China