in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faraministan kasar Sin ya yi kira da a mai da muhimmanci wajen zamanintar da noma domin dorewar tattalin arziki
2015-02-16 14:25:04 cri

A cewar faraministan kasar Sin Li Keqiang, akwai wata bukatar gaggawa ta zamanintar da aikin gona domin tabbatar wata bunkasuwa mai dorewa da cigaba cikin karko.

Kawo kimiyya da fasaha cikin aikin noma, wani babban aiki ne dake bukatar bayyana muhimmanci da darajar yankunan kasar Sin daban daban, in ji mista Li a cikin wani rahoto mai taken "gaggawata zamanintar da aikin gona ta hanyar amfani da yunkurin kawo sauye sauye da kirkirowa".

Wannan rahoton da ya samo tushe daga wani jawabin da mista Li Keqiang ya gabatar a cikin watan Disamban bisa taken cigaban karkara, da za'a fitar a ranar Litinin cikin mujallar Qiushi wato "neman gaskiya", wata mujallar kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (PCC).

Tare da bada kwarin gwiwa ga dukkan fannonin gudanar da ayyukan noma iri daban daban bisa matakai madaidaita, mista Li ya yi kira ga karin tallafin siyasa da kudi mafi girma ga ayyukan noma baki daya.

A cewarsa, ya kamata cigaban birane ya kawo kyautatuwar kasuwancin karkara da kara kudin shiga na manoma. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China