in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban kasar Sin ya gana da babbar jami'ar kasar Ghana
2015-07-17 21:40:05 cri

Mataimakin shugaban kasar Sin Mr Li Yuanchao, ya gana da minista mai kula da harkokin diplomasiyya da dunkulewar Afrika ta kasar Ghana Madam Hannah Tetteh a nan birnin Beijing.

Yayin ganawar ta su, madam Hannah Tetteh ta ce Sin sahihiyar abokiya ce ga kasar Ghana, ta na kuma matukar godiya ga irin taimakon da Sin ke samarwa a fannin raya tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar al'ummar Ghana.

Kaza lika mahukuntan Ghana na fatan kara fadada hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin samar da tsabtaccen makamashi da sauran su, tare kuma da sa kaimi ga inganta ci gaban hadin gwiwar sassan biyu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China