Mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao a ran 18 ga wata a nan birnin Beijing ya gana da kungiyar duba aiki ta ma'aikatan hukumar kungiyar SPLM ta kasar Sudan ta kudu dake karkashin jagorancin Kom Kom Geng, inda Li Yuanchao ya yi nuni da cewa, Sin na dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakaninta da kasar Sudan ta kudu, kuma tana fatan samun karin amincewa da juna a fannin siyasa tare da hadin gwiwa da zurfafa musayar al'adu.
Ya ce Jam'iyyar kwaminis ta Sin tana fatan kara mu'amala da kungiyar SPLM a dukannin fannoni ta yadda za su sa kaimi ga bunkasa dangantakar hadin gwiwa tsakaninsu yadda ya kamata.
A nasa bangare, Kom Kom Geng ya nuna cewa, kungiyar SPLM na fatan yin nazari da kuma yin amfani da fasahar da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta samu wajen gudanar da ayyukan jam'iyya da ma kasar, tare kuma da sa kaimi ga yin musayar ra'ayi a fannin zuba jari, ba da ilmi da al'adu. (Amina)