A yayin shawarwarin da suka gudanar a jiya Laraba a nan birnin Beijing, Mr. Li Yuanchao ya bayyana cewa, Sin da Tanzania abokai ne a kowane yanayi, kuma kasar Sin tana fatan ci gaba da kwazo tare da kasar Tanzania, wajen aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito a kan su.
Kaza lika Sin na da burin kara hadin gwiwa da kasar a fannonin ayyukan more rayuwa, da makamashi, da harkar sufurin jiragen sama, da gina yankin masana'antu da dai sauransu, ta yadda hakan zai taimaka, wajen inganta dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakanin sassan biyu.
A nasa bangare, Bilal ya bayyana cewa Tanzania, na dora muhimmanci kan zumuncin dake tsakaninta da kasar Sin, kuma tana da burin koyi daga fasahohin Sin a bangaren yin kwaskwarima, da bude kofa. Tana kuma maraba da kamfanonin Sin a fannin zuba jari. (Zainab)