Mr Li wanda ya tabo tarihin hadin gwiwar kasashen biyu yayin jawabinsa, ya yi fatan sassan biyu za su yi mafani da bikin cika shekaru 35 da kulla huldar diflomasiya wajen daga dangantakar da ke tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi.
Ya ce, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin za ta kara karfafa musaya tsakaninta da jam'iyyar ZANU-PF don bunkasa ci gaban da ke tsakanin kasashen biyu.
A jawabinsa Mnangagwa wanda har ila shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar ZANU-PF mai mulki a kasar ta Zimbabwe ya ce, kasashen biyu da kuma jam'iyyunsu za su ci gaba da karfafa hadin gwiwar da ke tsakanisu ta yadda za ta kara fadada. (Ibrahim)