A ranar Talata, mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao ya gana da firaminsitan kasar Uganda Amama Mbabazi a birnin Beijng na kasar Sin.
A yayin ganawar, Li ya bayyana cewa, kasar Sin da kasar Uganda sun fuskanci wata babbar dama ta cudanya a fuskar hadin gwiwa, kuma kasar Sin a shirye take ta kara dankon aminci irin na siyasa da kuma fadada hadin gwiwa tsakaninta da kasar Uganda domin a samu kyakyawan sakamako.
Mbabazi har wa yau shi ne sakatare janar na jam'iyyar National Resistance Movement (NRM) mai mulki a kasar Uganda.
Li ya ci gaba da cewa, yana fatan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC) da jamiyyar NRM za su kara yin musayar shawarwari kan harkokin shugabanci don cimma wadata.
Mbabazi ya nuna cewar, yana burin ganin karin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da ma tsakanin jam'iyyun biyu. (Lami)