in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shguaban kasar Sin ya gana da takwaransa na Equatorial Guinea
2013-11-13 20:56:00 cri

A ranar 13 ga wata a nan birnin Beijing, mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao ya gana da mataimakin shugaba na biyu na kasar Equatorial Guinea Mista Teodoro Nguema Obiang Mangue.

A ganawarsu, Mista Li yana fata bangarorin biyu za su zurfafa amincewar juna a fannin siyasa, da habaka hadin kansu a fannonin man fetur, da ba da rancen kudi, da injiniyoyi, da horar da ma'aikata da dai sauransu, ta yadda za a iya daga dangantakar abuta da hadin kai ta gargajiya da ke tsakanin Sin da Equatorial Guinea a wani sabon matsayi.

Mista Mangue ya fadi cewa, kasashen Equatorial Guinea da Sin su abokai ne na gaskiya, kuma yana fatan bangarorin biyu za su inganta hadin kansu irin na moriyar juna a fannonin ayyukan more rayuwar al'umma, da man fetur, da kiwon lafiya da dai sauransu, a kokarin samar da alheri ga jama'ar kasashen biyu.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China