Yayin ganawar ta su, Kikwete ya bayyana cewa, jama'ar kasarsa da ta kasar Sin suna da zumunci na tsawon lokaci, kuma abokai ne na hakika. Don haka ya yi fatan za a kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, da kara zuba jari a fannonin iskar gas, wutar lantarki, aikin gona, zaman rayuwar jama'a, mashigin teku da dai sauransu. Kana ya yi fatan kara yin mu'amala a tsakanin jam'iyyun kasashen biyu don inganta dangantakarsu zuwa wani sabon matsayi.
A nasa bangare, Li Yuanchao ya bayyana cewa, a cikin shekaru 50 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Tanzania, an samu nasarori da dama a dukkan fannoni, kuma sassan biyu na nuna goyon baya ga juna kan batutuwan dake shafar moriyarsu, tare da kasancewa abokai a kowane hali. Ya ce kasar Sin tana burin yin hadin gwiwa tare da kasar Tanzania, da aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito kan su, da rike damar samun bunkasuwa, da kara yin mu'amala, da kara yin hadin gwiwa mai ma'ana da cimma moriyar juna don daga dangantakar abokantaka a tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)