A lokacin ganawar Li Yuanchao ya ce, a cikin shekaru sama da 50 da suka gabata, bayan da Sin da Masar suka kulla dangantakar diflomasiya an gudanar da zumunci tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, don haka kasar Sin take girmama zabin kasar jama'ar Masar game da tsarin siyasa da hanyar samun bunkasuwar su. Ya ce Sin tana kuma mai da hankali sosai game da dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin kasashen biyu tare da fatan kiyaye da fadada mu'amala da hadin gwiwa da kasar ta Masar.
A nasa bangare shi ma Nabil Fahmi ya yi bayani game da sabon yanayin da ake ciki a kasar Masar, inda ya ce, raya dangantakar da ke tsakaninta da Sin, ya zama zaben da Masar ta yi, kuma yana fatan ci gaba da inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da zurfafa mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin su daga dukkan fannoni .(Bako)