A lokacin ganawar, Mr Li ya nuna cewa, wannan shekara da muke ciki ta kasance cikon shekaru 35 da kasashen Sin da Amurka suka kafa dangantakar diplomasiyya. Don haka ya kamata sun tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kuma nacewa ga bin hanyar raya sabuwar dangantakar tsakaninsu.Ya ce hakan ya hada da habaka hadin kai mai yakini a dukkan fannoni, da kuma daidaita bambancin ra'ayi da wasu manyan batutuwan da suka fi jawo hankalinsu, sannan da sa kaimi ga yin mu'ammala a dukkan fannoni, domin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.
A nasa bangare, William Burns ya bayyana cewa, dangantaka mai kyau tsakanin kasashen biyu ba ma kawai ta haifar da alfanu ga kasashen ba, har ma ya amfanawa sauran kasashen duniya. A cewar shi Amurka ta dukufa wajen sa kaimi ga kasashen biyu da su kara hada kai a dukkan fannoni,da yin iyakacin kokarin kafa sabuwar dangantaka a tsakaninsu. (Amina)