in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi shawarwari tsakanin manyan shugabannin kasar Sin da Sudan
2013-06-29 16:29:13 cri

Mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta Sin, kana mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao, a ran 28 ga wata a nan birnin Beijing, ya yi shawarwari da mataimakin shugaban jam'iyyar NCP ta kasar Sudan, kuma mai ba da taimako ga shugaban kasar, Nafia wanda ya halarci shawarwari tsakanin shugabannin jam'iyyun dake rike da shugabanci na kasar Sin da Sudan karo na biyu.

Li Yuanchao ya ce, jam'iyya da gwamnatin kasar Sin sun dora muhimmanci sosai kan dankon zumunci dake tsakanin kasashen biyu, kuma suna hangen nesa kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Yin shawarwari tsakanin jam'iyyun dake rike da shugabancin kasashen biyu ya kasance wani muhimmin dandali da zai kara inganta tuntubar juna, da kuma gaggauta hadin gwiwa tsakaninsu.

Ya kamata, kasashen biyu su zurfafa shawarwarin tsakanin jam'iyyunsu ta yadda za a bunkasa dangantakar sada zumunci a dukkan fannoni tsakaninsu.

A nashi bangare, Nafia ya ce, Sin sahihiyar kawa ce ga kasar Sudan, yana fatan ganin kara amincewa da juna a fannin siyasa da zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu ta wannan shawarwari tsakanin jam'iyyun biyu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China