Yayin da Liu Yandong ke ganawa da madam Zuma, ta bayyana cewa, kungiyar AU ta taka muhimmiyar rawa wajen daidaita batutuwan kasashen Afrika da na kasashen duniya, har ma take shugabantar kasashen Afrika wajen hada kai, ta yadda za su farfado.
Ta ce kasar Sin na mai da hankali game da alakar da ke tsakaninta da kungiyar AU. Liu ta kara bukatar bangarorin biyu, da su kara yin mu'amala, da zurfafa hakikanin hadin gwiwa a fannonin samar da muhimman ababen more rayuwa, da raya aikin kwadago, da kiwon lafiya, da kimiyya da fasaha da raya harkokin mata. A cewar ta, ya zama dole bangarorin biyu su inganta hadin gwiwa wajen aikin samar da zaman lafiya da karko, da sauran manyan batutuwan duniya, don kiyaye moriyar kasashe masu tasowa.
A nata tsokaci madam Zuma, bayyana godeyarta ta yi da irin goyon baya, da taimako da Sin ta bayar wajen aikin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Afrika, tana mai cewa, kasashen Afrika za su koyi fasahohi da dama da kasar Sin take da su, don cimma burin wanzar da zaman lafiya, da bunkasuwa da hadin gwiwa a nahiyar Afrika, kuma kasashen Afrika suna sa ran karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni daban daban.
A dai wannan rana, Liu Yandong ta kuma gana da mataimakin firaministan kasar Habasha Demeke Mekonnon.(Bako)