Bisa labarin da ofishin kula da harkokin ketare na kungiyar EU ya fitar, an ce, wannan lokacin na ziyarar babbar wakiliyar EU a kasar Cuba, wani muhimmin lokaci ne na yin shawarwari tsakanin kungiyar AU da kasar Cuba, a tsawon wannan ziyara, kuma madam Mogherini za ta gana da wasu jami'an kasar Cuba, ciki hada da ministan harkokin wajen kasar Celcy Rodriguez domin tattauna harkokin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu da dai sauran batutuwa.
Haka kuma, madam Mogherini ta bayyana cewa, kungiyar EU na sa ran ciyar da dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu gaba, kungiyar na mai da hankali sosai kan ci gaban kasar Cuba, da kuma cigaban dangantakar dake tsakanin kasar Cuba da sauran kasashen duniya, domin wadannan hanyoyi na bunkasuwa za su samar wa kungiyar EU da kasar Cuba sabbin damammakin neman ci gaba.
A cikin watan Disamban shekarar da ta gabata, shugaban kasar Amurka Barack Obama da shugaban kasar Cuba Raul Castro sun ba da jawabai cewa, kasashen biyu za su yi shawarwari kan farfado da dangantakar diflomasiyyar dake tsakanin kasashen biyu, wasu kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sun yi maraba da ci gaban dangantakar dake tsakanin kasashen nan biyu. (Maryam)