AU ta ba da wata sanarwa a ranar Juma'a cewa, a yayin taronta karo na 497 da aka yi a ranar Alhamis, kwamiti mai kula da zaman lafiya da tsaro (PSC) na kungiyar ya tattauna kan harin da aka kai garin Garissa dake arewa maso gabashin kasar Kenya a ran 2 ga wata.
Ban da wannan kuma, kwamitin ya yi tir da wannan hari, inda kungiyar Al-Shabaab ta kutsa kai cikin jami'ar Moi da ke Garissa tare da kashe dalibai da ma'aikata 148, da kuma jikkata wasu da dama.
Haka zalika, a cewar kwamitin, ganin yadda halin da ake ciki ke kara tsananta dalilin ta'addanci, ya kamata a kara karfin yaki da ta'addanci bisa ka'idar kungiyar AU da kasa da kasa dake da nasaba da wannan lamari. Ban da haka kuma, ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar AU da abokanta da su yi iyakacin kokarin tinkarar ta'addanci, tare kuma kara hadin gwiwa tsakaninsu a wannan fanni.
Dadin dadawa, kwamitin nan na kula da zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar Afirka ya sake nanata alkawarin daukar matakan da suka dace, ta yadda kwamitinsa na yaki da ta'addanci zai iya aiwatar da ayyukansa yadda ya kamata. (Amina)