Da yake gabatar da takardar, Mr. Kuang ya bayyana cewa, dangantaka tsakanin Sin da kungiyar AU, wani muhimmin bangare ne cikin dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka. Kana a matsayinta na muhimmiyar tuta dake jagorantar ci gaban nahiyar Afirka, AU na taka rawar gani a fannonin raya tattalin arziki, da na zamantakewar al'umma, da kuma yunkurin tabbatar da zaman lafiya da tsaron nahiyar Afirka.
Ya ce shi da sauran abokan aikinsa, za su sanya kwazo wajen karfafa mu'amala da hadin gwiwa tsakanin Sin da kungiyar a dukkanin fannoni, kana zasu sa kaimi ga tabbatar kudurorin da shugabannin Sin, da shugabannin kasashen Afirka suka cimma, ta yadda dangantaka tsakanin sassan biyu za ta haifar da gudummawa ga bunkasar Sin da kasashen Afirka baki daya.
A nata bangare, uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma, ta yi maraba da zuwan mista Kuang, tana mai yabawa kasar Sin game da samar da wakilci a kungiyar AU.
Daga nan sai ta jinjinawa kasar Sin bisa taimakon da take bayarwa ga bunkasar kungiyar AU, da tattalin arziki, da zamantakewar al'ummar kasashen Afirka cikin dogon lokaci. Ta ce, hukunar kungiyar AU da ita kanta, suna fatan kara zurfafa dankon zumunci tsakaninsu da kasar Sin. (FATIMA)