in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron kolin AU karo na 24
2015-02-01 16:49:31 cri

Jiya ranar 31 ga watan Janairu, a birnin Addis Abeba, hedkwatar kasar Habasha, an rufe taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU karo na 24, wanda aka kwashe kwanaki 2 ana yinsa.

A yayin bikin rufe taron, shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe kuma shugaban kungiyar AU a wannan zagaye ya yi jawabi da cewa, bisa kokari da goyon baya da kungiyar AU da jama'ar Afirka suke yi tare, dukkan mambobin kungiyar za su hada kai su kafa wata nahiyar Afirka mai zaman lafiya da wadata, inda kuma za a mayar da dan Adam a gaba da kome.

Shugaba Mugabe ya kara da cewa, a yayin taron an zartas da shirin raya Afirka nan da shekarar 2063, tare da amincewa da kafa wata cibiyar yin rigakafin cututtuka ta Afirka. sa'an nan mahalarta taron sun tattauna kan yadda za a bai wa mata iko da raya nahiyar Afirka da dai sauran batutuwa. Sun cimma daidaito a fannoni da dama, alal misali, mata da kananan yara, babban arziki ne ga nahiyar Afirka. Wajibi ne a bai wa mata iko. Kara azama wajen kawar da bambanci a tsakanin mata da maza, lamarin da zai taimakawa Afirka wajen daidaita albarkatunta yadda ya kamata, ta yadda za a samu saurin bunkasuwar nahiyar.

A yayin taron kuma, mahalarta taron sun yi tattaunawa kan warware rikicin shiyya-shiyya, yaki da cutar Ebola, yaki da ta'addanci, hadewar shiyya-shiyya da dai sauransu. Har wa yau sun nuna kulawa kan halin da ake ciki a kasashen Mali, Sudan ta Kudu, Somaliya, Libiya a fannonin tsaro da yaki da 'yan ta'adda.

An bude taron shugabannin kungiyar AU ne a ranar 30 ga watan jiya, bisa taken "bai wa mata iko da tsara shirin raya Afirka nan da shekarar 2063" A lokacin taron, shugabanni da wakilai daga kasashe fiye da 50 mambobin kungiyar sun tattauna manufar raya Afirka cikin dogon lokaci da bai wa mata iko da kawar da bambanci a tsakanin mata da maza da dai makamantansu. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China