in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron koli na AU zai mai da hankali kwarai ga kare hakkin mata
2015-01-28 11:06:26 cri

Za a gudanar da taron koli karo na 24 na kungiyar tarayyar Afrika ta AU, daga ranar 30 zuwa 31 ga watan nan na Janairu, a birnin Addis Ababan kasar Habasha. Taron da ake sa ran shugabanni ko wakilan kasashe mambobin kungiyar 50 za su halarta.

Ya yin taron mahalartan sa za su tattauna kan wasu batutuwa dake jawo hankalin kasashen nahiyar, ciki har da raya Afirka cikin dogon lokaci, da kare hakkin 'yan mata dake nahiyar, da samar da daidaito tsakanin mata da maza da dai sauransu.

Kungiyar ta AU dai na kara kwazo wajen raya Afrika a shekarun baya bayan nan, ta hanyar aiwatar da manufar kawo karshen yake-yake a nahiyar kafin nan da shekarar 2020, da kawar da yunwa kafin shekarar 2025, da ma batun aiwatar da tsarin cimma muradun nahiyar nan da shekarar 2063.

Kaza lika AU na da burin samar da sabuwar Afrika, cikin yanayi na lumana da wadata nan da shekaru 50 masu zuwa. Ya yin da wannan tsari zai zamo babban jigo da za a tattauna yayin taron na wannan karo.

An ba da labari cewa, yayin taron, wakilai daga MDD, da na sauran kungiyoyin kasa da kasa, za su gudanar da shawarwari tare da wakilan AU, kan wasu batutuwa masu alaka da rayuwar 'yan mata, kuma za su mai da hankali kan matakan kawar da ra'ayin muzgunawa mata, da batun kiyaye hakkin su da dai sauransu.

Dadin dadawa, shugabannin kasashe mambobin AU, za su tattauna kan wasu batutuwa bisa ajandar taron, ciki hadda na kandagarkin barkewar cutuka, da tabbatar da tsaron nahiyar, da samun bunkasuwa cikin dogon lokaci, tare da kiyaye muhalli, da hadin gwiwa wajen samun bunkasuwar Afirka baki daya, da dai sauran muhimman batutuwa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China