A jiya ne MDD da kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU suka kaddamar da cibiyar nazarin dokoki kasa da kasa wato AIIL a birnin Arusha da ke arewacin kasar Tanzaniya.
A jawabinsa yayin bikin bude cibiyar, mataimakin ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na kasar Tanzaniya Mahadhi Juma Maalim ya ce, cibiyar wata muhimmiyar kafa ce wajen bunkasa nahiyar.
Ya ce, babban kalubalen da nahiyar Afirka ke fuskanta, shi ne yadda za ta bunkasa karfinta na samun bunkasuwa a dukkan matakai ta yadda za a samu nasarar kawar da talauci tare da samun dawwamammen ci gaba,
Ko da yake a cewarsa, yanzu ana samun zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a nahiyar, bayan da ta fuskanci matsalolin siyasa, harkokin rayuwa da tattalin arziki a shekarun baya. Amma kuma gibin da ke akwai a dukkan matakai ya gurgunta kokarin nahiyar na samun ci gaba a wadannan fannoni.
A nasa jawabin mutumin da ya kirkiro cibiyar ta AIIL mai shari'a Abdulqawi Yusuf ya ce, cibiyar za ta taka muhimmiyar rawa a nahiyar wajen kara yabawa da kuma fahimtar dokokin kasa da kasa, baya ga samar wa nahiyar kwararrun ma'aikata wadda hakan zai rage irin dogara da nahiyar ta Afirka ke yi kan kwararru na ketare wajen tafiyar da harkokinta.(Ibrahim)