Sidikou wanda ke jagorantar tawagar wanzar da zaman lafiyar kungiyar ta AU a Somaliya ko AMISOM a takaice, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labaru da ya gudana a jiya Jumma'a, yayin babban taron AUn karo na 24, dake gudana a birnin Addis Ababan kasar Habasha.
Ya ce goyon bayan da kasar Sin ke baiwa kungiyar AU da tawagar AMISOM a fannin shimfida zaman lafiya, ya nuni ga kasancewarta aminiya ga nahiyar Afirka baki daya.
Kaza lika Sidikou ya jinjinawa kamfanonin kasar Sin bisa sha'awar da suka nuna, na zuba jari a Somaliya, baya ga tallafin da Sin din ke baiwa tawagar AMISOM. Ya ce Sin na daya daga cikin kasashen da suka fara bude ofishinsu a birnin Mogadishu, fadar gwamnatin Somaliya. (Saminu Hassan)