Dangane da lamarin, mataimakin shugaban Asusun zaman lafiya na Carnegie Douglas Parr ya bayyana cewa, ko da a halin yanzu, ana fuskantar wasu sabani a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka kan batutuwan dake shafar Tekun Kudu na kasar Sin da kuma tsaron intanet da dai sauransu, amma Fan Changlong ya kai ziyarar aiki a kasar Amurka bisa lokacin da aka tsara, ya nuna ci gaban shawarwarin harkokin soja dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, da kuma ci gaban dangantakarsu kan harkar soja, lamarin zai taimaka wajen yin rigakafi kan matsalolin da mai iyuwa za su bullo a nan gaba.
Haka kuma, shugaban cibiyar nazarin manufofin diflomasiyya ta kungiyar Brookings Michael O'Hanlon ya bayyana cewa, ko da kasar Sin da kasar Amurka ba za su kawar da sabanin dake tsakaninsu kan batutuwan Tekun Kudu da kuma tsaron intanet ba sakamakon ziyarar aiki ta wannan karo, amma babu shakka shawarwarin da suka yi kan batutuwan zasu ba da babban taimako. (Maryam)