A jiya ne hukumar kula da kare hakkin dan Adam ta MDD ta tantance yadda kasar Amurka take kare hakkin dan Adam a kasar, inda ta ba da shawara da kuma suka kan wasu matsalolin da Amurka ke fuskanta, kamar gudanar da shari'a ba ta hanyar da ta dace ba, nuna bambanci a tsakanin maza da mata, nuna bambancin addinai, da tsakanin al'umma, azabtar da wadanda ake tsare da su da kuma batun gidan kurkuku nan na Guantanamo da dai sauransu.
Dangane da lamarin, Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, yadda hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD ta nazarci yadda Amurka ta ke tafiyar da batun kare hakkin dan adam a cikin kasar ta sake shaida cewa, babu wata kasa da za a ce, ba ta da wani tabo dangane da bayananta na kare hakkin bil Adama.Wajibi ne ta rika kyautata bayananta daga lokaci zuwa lokaci.
Madam Hua ta kara da cewa, kasar Sin na fatan kasashen da aka nazarci nasu batun za su karbi shawarar da aka ba su ba tare da nuna girman kai ba, ta yadda za su yi kokarin warware matsalolin da suke fuskanta na kiyaye hakkin dan Adam, da kuma kyautata yadda suke kiyaye hakkin dan Adam a kasashen nasu.
Hua ta ci gaba da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da hada kai da kasashen duniya wajen kara azama kan tantance yadda kasashen duniya suke kiyaye hakkin dan Adam cikin adalci kuma bisa yadda abubuwa suka kasance. (Tasallah Yuan)