Mista Qin ya fadi haka ne a yau yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, a lokacin da ake masa tambaya cewa, a ganin wasu Amurkawa, yayin da kasar Sin ta zargi kasar Amurka dangane da gana wa fursunoni azaba a gidan kurkuku na Guantanamo da kuma yadda 'yan sandan kasar suke harbe Amurkawa-bakaken fata, Amurka ta ci gaba da sukar kasar Sin kan yadda take aiwatar da dokoki da kuma kiyaye hakkin dan Adam. Mene ne ra'ayin kasar Sin kan hakan?
Mista Qin ya ce, in aka tantance yadda kasashen Sin da Amurka suke kiyaye hakkin dan Adam, kasar Sin na ganin cewa, ko wace kasa na bukatar ci gaba da kokari a wannan fanni. Kasar Sin ta san yadda take tafiyar da harkokinta a wannan fannin sosai, kuma ba ta son koya wa wasu kasashe hanyoyin kiyaye hakkokin dan Adam ba. (Tasallah)