A yayin ganawarsu, Xi Jinping ya bayyana cewa, a halin yanzu, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka na bunkasa cikin yanayi mai kyau, don haka ya jaddada cewa, ya kamata a karfafa fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, warware sabanin dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, ta yadda za a iya habaka hadin gwiwar moriyar juna tsakanin kasashen biyu, har ma a tsakanin kasa da kasa da kuma shiyya-shiyya.
A nasa bangaren Kissinger ya ce, gina sabuwar dangantakar manyan kasashe a tsakanin Sin da Amurka ya dace da moriyar kasashen biyu, ya kuma dace da ci gabansu, haka kuma, ya yi imani cewa, ziyarar aikin da shugaba Xi Jinping zai kai a kasar Amurka za ta kasance muhimmiyar ziyara cikin tarihi, ya kuma nuna fatan alheri ga Mr. Xi kan cimma nasarar wannan ziyara. (Maryam)