in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi ya gana da mai taimakawa shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaro
2015-02-26 15:34:01 cri
Mamban majalisar harkokin kasar Sin Yang Jiechi, ya gana da jami'a mai taimakawa shugaba Barack Obama na Amurka kan harkokin tsaro Susan Rice.

Yayin ganawar tasu a jiya Laraba a birnin New York, jami'an biyu sun yi hasashen cewa ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai Amurka a watan Satumbar bana, za ta zamo mai babbar ma'ana, don haka suka nuna bukatar bangarori biyu su yi hadin gwiwa, wajen gudanar da shirye-shiryen tabbatar da nasarar ziyarar.

Yang Jiechi ya ce a kwanakin baya, shugaba Xi Jinping da takwaran sa na Amurka Barack Obama sun zanta ta wayar tarho, inda suka gabatar da ra'ayoyi game da inganta sabuwar dangantakar Sin da Amurka.

Ya ce kamata ya yi kasashen biyu su aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen su suka cimma matsaya a kan su, da shirya mu'amala tsakanin manyan jami'an kasashen biyu, da girmama juna kan batutuwan da suke sa lura. Sauran fannonin sun hada da fadada hadin gwiwa a dukkan fannoni, da kara yin hadin gwiwa kan manyan batutuwan duniya da na yankuna, da warware matsaloli yadda ya kamata, domin sa kaimi ga kara samun ci gaban dangantakar dake tsakaninsu a sabuwar shekara.

A nata bangare, Rice ta bayyana cewa, kasar Amurka na fatan aiwatar da ra'ayoyin da shugabannin biyu za su cimma daidaito kan su, da batun kara yin hadin gwiwa da mu'amala a tsakaninta da kasar Sin a dukkan fannoni, da tinkarar kalubalen duniya da na yankuna tare, da warware matsalolin dake tsakaninsu ta hanya mafi dacewa, da kuma kiyaye bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China