Da yammacin yau Litinin 30 ga wata ne firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da manzon musamman na shugaban kasar Amurka, kuma ministan kudin kasar Jacob J. Lew.
A yayin ganawar, mista Li ya ce, kyakkyawar huldar da ke tsakanin Sin da Amurka na dacewa da moriyarsu duka, kuma yana taimakawa kiyaye zaman lafiya, da kwanciyar hankali da wadata a nahiyar Asiya, da yankin tekun Pacific, da ma duk duniya baki daya.
Ya ce ziyarar aiki da shugaba Xi Jinping zai gudanar a Amurka a watan Satumba mai zuwa, za ta kara bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen 2. Kaza lika ya ce nan gaba, kamata ya yi bangarorin 2 su ingantawa da juna, da hadin gwiwarsu, tare da kara tuntubar juna a manyan al'amuran shiyya-shiyya da na kasa da kasa.
A nasa bangaren, mista Lew ya ce, kasar Amurka na sa ran ziyarar Xi Jinping a kasar a watan Satumbar dake tafe. Ta na kuma maraba da kasar Sin wajen taka rawa a fannin kyautata ababen more rayuwar jama'a a Asiya, da ma inganta hadin gwiwar da ke tsakaninsu a wannan fanni. (Tasallah Yuan)