Mr. Cui ya bayyana hakan ne yayin da ya halartar taron kamfanonin Sin masu jari a kasar Amurka na shekarar 2015, wanda babbar kungiyar cinikayyar Sin da Amurka suka gudanar a daren ranar jiya Litinin.
Ya ce kyakkyawan fatan nasa na da alaka da nasarorin da Sin ta samu, a fannin bunkasa tattalin arziki yadda ya kamata, kana Sin na tsaiwa tsayin daka wajen aiwatar da manufar bude kofa. Sauran sun hada da aikin yin kwaskwarima, da gudanar da harkokin kasa bisa doka, da kuma yunkurin samu babban ci gaba a fannin kafa sabuwar dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Amurka.
Haka zalika Cui Tiankai ya ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyara kasar Amurka a watan Satumbar bana, matakin da zai kara kaimi ga kasashen biyu a bangaren kara fahimtar juna, da zurfafa hadin gwiwarsu. Haka kuma ziyarar shugaba Xi zai kara wa bangarorin masana'antu da na cinikayyar kasashen biyu kwarin gwiwa wajen nuna farin ciki game da wannan kyakkyawar makoma ta hadin gwiwar kasashen biyu. (Zainab)