in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron farko na hadin gwiwar Sin da Amurka kan hana yaduwar makaman kare dangi
2014-11-03 14:29:29 cri
An gudanar da taron hadin gwiwa irinsa na farko tsakanin kasashen Sin da Amurka a nan birnin Beijing, game da hana yaduwar manyan makaman kare dangi.

Mr. Li Yang wanda shi ne mataimakin shugaban sashen kula da harkokin makaman soji a ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ne ya jagoranci tawagar kasar ta Sin yayin taron, yayin da kuma babban mataimaki ga ministan kula da tsaron kasa da kasa, da hana yaduwar manyan makamai a ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka Van Diepen, ya shugabanci tawagar Amurka.

Yayin taron tattauna manyan tsare-tsare da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka zagaye na 6 da aka yi a watan Yunin da ya shude ma dai, kasashen biyu sun cimma daidaito kan kafa rukunin hadin gwiwa, na hana yaduwar manyan makaman kare dangi a tsakaninsu.

Wannan ne dai karo na farko da kasar Sin ta shiga irin wannan tsarin hadin gwiwa tare da wasu manyan kasashen duniya, matakin da ke da nufin kara fadada mu'amala, da hadin gwiwa, da kawar da bambance-bambance a tsakanin Sin da Amurka a wannan fanni.

Kaza lika tsarin zai taimaka matuka wajen kara bunkasa fahimtar juna tsakanin Sin da Amurka a fannin tsaron kasa, da kafa sabuwar dangantaka tsakaninsu, da kuma sa kaimi ga inganta aikin hana yaduwar manyan makamai a fadin duniya.

Kuni dai gwamnatin kasar Sin ta bayyana kin amincewarta da duk wane mataki na yaduwar manyan makamai, ta kuma shiga hadin gwiwar sauran kasashen duniya, wajen hana yaduwarsu, baya ga kokarin da take yi na sauke nauyin dake wuyanta game da cika alkawarunta ga duniya baki daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China