Kaza lika jakadan ya ce Sin na fatan kasashen da wannan batu ya shafa, za su dauki matakan da suka dace wajen warware wannan matsala ta hanyar diplomasiyya.
Cui Tiankai ya yi nuni da cewa, Amurka ta dade tana yin baki biyu game zargin kasar Sin na gudanar da aikin shata yankunan kasa a kudancin tekunta.
Ya ce kasar Sin ba ta yi irin wannan aikin a wasu kasashe na daban ba, duk da cewa a baya wasu kasashen sun dauki irin wannan mataki a kan kasar ta Sin, kuma kasar Amurka ba ta taba zargin wadancan kasashen ba ko kadan. (Zainab)