in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake bude babban asibitin Luanda a Angola
2015-06-09 19:35:42 cri
A jiya Litinin ne, bayan da aka yi masa gyara da kuma daga matsayinsa, aka sake bude babban asibitin Luanda na kasar Angola, wanda kasar Sin ta ba da taimako wajen gina asibitin, haka kuma, a wannan rana, gwamnatin kasar Angola ta shirya wani kasaitaccen bikin bude asibitin.

A yayin bikin, ministan harkokin kiwon lafiya na Luanda Jose Van Dunem ya nuna godiya matuka ga gwamnatin kasar Sin dangane da babban taimako da ta samar wa kasar Angola wajen kyautata yanayin aikin jinya da kiwon lafiya na kasar, a madadin shugaban kasar Angola Jose Eduardo Dos Santos da kuma gwamnatin kasar. Ya ce, a halin yanzu, asibitin ya kasance mafi girma, da kuma kayayyakin jinya masu inganci cikin asibitocin kasar, wanda hakan zai kyautata yanayin kiwon lafiya da kuma taimakawa jama'ar kasar yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China