Kulab na wasannin wato kulab K.K. tana yankin kudancin birnin Luanda na hedkwatar kasar, kuma fadin filin kulab din ya kai murabba'in mita dubu 130.Kamfanin CITIC na kasar Sin ba ma kawai ya fasalta wannan kulab, har ma ya gina filayen wasan kwallon kafa guda 2 da fadinsu ya kai murabba'in mita dubu 15.
Bayan da kamfanin CITIC ya fara aiki a kasar Angola cikin shekaru sama da 5 da suka gabata, ya samar da guraben ayyukan yi sama da dubu 10 a wurin, inda suka bude makarantun horas da ma'aikatan gine-gine, da horar da ma'aikata ba tare da biyan ko sisi ba, kuma ya tashi tsaye don gina hanyoyin dogo, da gidaje, da haka rijiyoyi, da gina makarantu a kyautu. Haka kuma, wannan kamfani ya ba da kudi don raya wasannin kwallon tebur, da kwallon raga, da wasan dambe da sauransu, abun da ya sa Angola ta cimma burin samun lambobin yabo a wasannin kwallon tebur na cin kwafin Afrika.(Bako)