Vicente wanda ya bayyana hakan ranar Jumma'a 27 ga wata, yayin da yake tsokaci gaban mahalarta babban taron MDD na shekara-shekara da ke gudana a hedkwatar Majalissar dake birnin New York, ya ce kasarsa na matukar imani da tasirin da MDD ke da shi, wajen tabbatar da yanayin zaman lafiya, da daidaito, tare da kwarewar samar da kandagarkin barkewar tashe-tashen hankula a dukkanin sassan wannan duniya.
A cewarsa taron na bana na zuwa ne a gabar da ake matukar bukatarsa, duba da irin halin rigingimu da dake addabar sassan duniya daban-daban.
Daga nan sai mataimakin shugaban kasar ta Angola ya nanata bukatar daukar dukkanin matakan da suka wajaba, wajen magance dimbin matsalolin dake addabar al'umma, ciki hadda batun yaduwar kananan makamai, da ayyukan ta'addanci, da fashin teku, da cinikayyar muggan kwayoyi, da kuma kangin talauci dake addabar al'ummun dake sassan duniya da dama. (Saminu Hassan)