in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar HCR ta kawo karshen kwashe 'yan gudun hijirar Angola dake Botswana
2013-11-03 16:55:25 cri
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dunkin duniya, HCR ta kawo karshen kwashe 'yan gudun hijira dake bukata na kasar Angola dake kasar Botswana, ta hanyar shirya jigilar karshe ta mutane 194, a cewar wata majiyar MDD a ranar Asabar.

HCR ta yi gargadin cewa kasashen da lamarin ya shafa sun bayyana karshen matsalar 'yan gudun hijirar kasar Angola a ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2012, amma kasar Botswana ta yi jira wannan shekara domin kula da wannan matsala da kanta.

Tsoffin 'yan gudun hijirar kasar Angola an ba su damar har zuwa wannan lokacin karshen watan Oktoba su koma gidajensu.

Ayarin wannan mako na kunshe da 'yan kasar Angola 461 da aka kwashe daga Botswana tun cikin watan Yunin shekarar 2012.

Yakin neman 'yancin kasar Angola daga uwar renonta kasar Portugal tsakanin shekarar 1961 da shekarar 1975, sannan kuma da yakin basasar har zuwa shekarar 2002 sun haddasa mutuwar dubun dubatar mutane da kuma tilastawa miliyan hudu kaura daga gidajensu, inda a cikin akwai 'yan gudun hijira dubu 550 wanda yawancinsu suka isa kasashen dake makwabtaka da Angola, a cewar wasu alkaluman MDD. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China