Bisa rahoton binciken da kamfanin ya yi ga kasar ta Angola, an ce tattalin arzikin kasar zai samu ci gaba cikin kyakkyawan yanayi, kuma karuwar tattalin arzikin kasar zai karu da kashi 6.8 bisa dari a shekarar nan da muke ciki, kari bisa yadda aka zayyana a kasafin kudi, wanda zai kai kashi 2 ko 3 bisa dari na ma'aunin tattalin arzikin kasar ko GDP.
Sai dai a hannu guda bisa hasashen da gwamnatin kasar ta Angola ta yi, za ta samu gibin kudi da kimanin kashi 4.9 bisa dari a bana, sabo da bambancin hasashen da kamfanin Moody's ya yi da kuma na gwamnatin kasar ta Angola game da farashin man fetur na kasa da kasa. Bisa hasashen da kamfanin na Moody's ya yi, farashin man fetur zai ci gaba da kasancewa kan dallar Amurka 106 ko wace ganga, sabanin hasashen gwamnatin kasar dake ganin farashin man fetur zai ragu zuwa dallar Amurka 98 kan ko wace ganga. (Maryam)