Ribas ya bayyana wa 'yan jarida cewa, wannan shiri bai takaita ga wata kasa ko kasar Sin kadai ba, mataki ne na binciken baki 'yan kasashen waje dake zaune a babban birnin kasar.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Angola ta sanar da cewa, a ranar Jumma'a 19 ga wata 'yan sanda sun binciki 'yan kasashen ketare 2161 da suka fito daga kasshen Portugal, Sin, Congo Kinshasa da dai sauransu, kuma 884 daga cikinsu na zaune a kasar ba bisa ka'ida ba.
Bayanai daga ofishin jakadancin Sin dake kasar Angola ya nuna cewa, a ranar 19 ga wata, 'yan sandan Angola sun kama Sinawa fiye da 300 ba tare da gudanar da wani bincike ba. Sai dai bayan da ofishin jakadancin Sin dake kasar Angola ya shiga-tsakani, an saki yawancin Sinawa bayan da suka gabatar da takardunsu na iznin zama.
Amma har yanzu, ana ci gaba da tsare Sinawa 13 da ba su da takardu iznin zama. Ofishin jakadancin Sin ya bukaci bangaren Angola da ya warware matsalolin da suka kunno ta hanyar matakan da suka dace. (Zainab)