Mr. Manuel ya bayyana hakan ne bayan da shugaban kasar Angola Jose Eduardo dos Santos, ya gana da shugaban bankin raya Afirka Donald Kaberuka a jiya Litinin.
Kaza lika Manuel ya kara da cewa, ana sa ran bankin na raya Afirka, zai samar da dala miliyan 600 a matsayin kashin farko na wannan rance a cikin watan Agusta mai zuwa, wanda kuma kasar ta Angola za ta yi amfani da shi a fannonin ginin ababen more rayuwa, da sufuri da kuma samar da makamashi.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, kamfanonin kasashen waje da dama sun nuna rashin jin dadi, na rashin damar samun dalar Amurka a bankunan kasar ta Angola, don haka ake fatan wannan rance da bankin na raya Afirka zai baiwa kasar Angola, zai sassauta wannan matsalar ta rashin samun kudaden kasashen waje da bankunan kasar ke fuskanta. (Zainab)