in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yu Zhengsheng ya gana da shugaban kasar Angola
2015-06-09 14:12:19 cri
Shugaban majalisar bada shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin Yu Zhengsheng, ya gana da shugaban kasar Angola José Eduardo dos Santos a Talatar nan.

Yayin zantawar ta su a nan birnin Beijing, Yu Zhengsheng ya bayyana cewa tun bayan kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Angola, kasashen biyu na sada zumunta da karfafa imincewa amincewa da juna, da nuna goyon baya da fahimtar juna kan batutuwan dake shafar moriyarsu, sun kuma zamo hakikanin hakikanan abokai.

Kaza lika dangantakar dake tsakanin Sin da Angola misali ce ne ta na cimma moriyar juna, da bunkasuwa tare cikin hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka.

A daya hannun majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin na fatan raya dangantakar hadin gwiwa tare da majalisar dokokin kasar Angola, da jam'iyyun kasar, da bangarori daban daban na al'ummar kasar, kana suna kara bunkasa mu'amala a fannonin bude kofa ga juna, da gudanar da kwaskwarima, da bunkasa tattalin arziki da dai sauransu. Har ila yau sassan biyu na sa kaimi ga kamfanonin kasar Sin masu zaman kansu wajen kara zuba jari a kasar ta Angola.

A nasa bangare, shugaba Santos ya bayyana cewa ana ci gaba da sada zumunta mai inganci tsakanin Angola da Sin. Kana kasar sa na godiya ga kasar Sin, bisa samar da gudummawa, da nuna goyon baya ga Angola, musamman a fannin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma, yayin da Angolar ke fatan karfafa hadin gwiwar ta da kasar Sin, da bunkasa mu'amala tsakanin majalisun dokokin kasashen biyu, don daga matsayin dangantakar su zuwa sabon matsayi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China